Faraministan kasar Mali Choguel Maiga ya gana da jakadan kasar Nijar dake kasar Mali
2024-06-25 13:30:22 CMG Hausa
A jamhuriyar kasar Mali, faraministan kasar Choguel Kokalla Maiga, ya gana tare da Abdou Adamou jakadan kasar Nijar dake Mali a ranar jiya 24 ga watan Junin shekarar 2024 a fadar faraministan kasar Mali dake birnin Bamako.
Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Wannan ganawa tare da faraministan kasar Mali ta gudana a gaban idon ministan harkokin wajen kasar Mali Abdoulaye Diop da mataimakansa. A yayin tattaunawar, jami’in diplomasiyyar kasar Nijar Abdou Adamou ya yi amfani da wannan dama domin kara jaddada godiya da yabo na al’ummar Nijar da hukumomin kasar kan goyon bayan da kasar Mali ta kawowa kasar Nijar tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Julin shekarar 2023 da biyo bayan takunkumin da kungiyar kasashen yammacin Afrika CEDEAO da kungiyar gamayyar tattalin arziki da kudi ta UEMOA kan Nijar, fiye da watanni bakwai, tare da barazanar daukar matakin soja kan sabbin hukumomin na wasu kungiyoyin shiyya-shiyya.
A nasa bangare, faraministan kasar Mali, Choguel Kokalla Maiga, a gaban tawagar kasar Nijar, ya sake jaddada goyon bayan al’ummar kasar Mali ga ’yan uwansu na kasar Nijar.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.