logo

HAUSA

Babban jami’in JKS ya ziyarci kasar Afrika ta Kudu

2024-06-25 10:41:41 CMG Hausa

Chen Wenqing, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kuma shugaban hukumar kula da harkokin siyasa da shari’a ta kwamitin kolin, ya ziyarci kasar Afrika ta Kudu daga ranar 20 zuwa 24 ga wata.

Yayin ziyarar, Chen Wenqing ya gana da sakatare janar na jam’iyyar ANC, Fikile Mbalula da tsohon shugaban kasar Kgalema Motlanthe.

Chen Wenqing ya kuma taya Afrika ta Kudu murnar gudanar da babban zaben kasar cikin nasara, inda jam’iyyar ANC ta samu nasarar da ta kai ga sake zaben shugaba Cyril Ramaphosa.

A cewarsa, karkashin kyakkyawan jagorancin shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa Cyril Ramaphosa, abota tsakanin Sin da Afrika ta Kudu ta ci gaba da yin karfi da zurfi, wadda ta bude wani sabon babi ta fuskar gina al’ummar Sin da Afrika ta Kudu mai makoma iri daya.

Bangaren Afrika ta Kudu ya jinjinawa nasarorin da aka samu daga hadin gwiwar kasashen biyu, ya kuma nanata kudurinsa na ci gaba da daukar Sin a matsayin abokiya tare da bayyana kudurin hada hannu da ita wajen kara inganta dangantaka bisa manyan tsare-tsare dake tsakaninsu. (Fa’iza Mustapha)