Xi Jinping zai halarci babban taron tunawa da cika shekaru 70 da fitar da wasu manufofi biyar na kasancewar kasa da kasa cikin lumana
2024-06-25 11:32:42 CMG Hausa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Hua Chunying ta sanar da cewa, a bana ake cika shekaru 70 da kasar Sin ta fitar da wasu muhimman manufofi biyar, kan kasancewar kasa da kasa cikin lumana, inda za ta gudanar da babban taron tunawa da ranar da sauran wasu jeren harkoki a ranar 28 ga wata a Beijing.
Ta kara da cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron tare da gabatar da muhimmin jawabi. (Murtala Zhang)