logo

HAUSA

Sin ta bukaci a zurfafa hadin gwiwa da musaya a fannin kimiyya da fasaha

2024-06-25 14:11:21 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira ga kasa da kasa su zurfafa musaya da hadin gwiwa a fannin kimiyya da fasaha.

Li Qiang ya yi kiran ne a birnin Dalian, lokacin da yake gabatar da jawabin bude zaman taron tattauna harkokin tattalin arzikin duniya da ake kira da taron Davos na lokacin zafi karo na 15.

Firaministan ya kuma yi kira ga kasa da kasa, su samar da kyakkyawan yanayi mai adalci ba tare da wariya ba, domin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha bisa kare ikon mallakar fasahohi. (Fa’iza Mustapha)