logo

HAUSA

Kungiyar Houthi ta Yemen ta dauki alhakin kai hari kan wasu jiragen ruwan dakon kaya 2

2024-06-24 10:43:54 CMG Hausa

Kungiyar Houthi ta kasar Yemen, ta dauki alhakin kai hari kan wasu jiragen ruwa 2 na dakon kaya, a tekun Maliya da yammacin tekun Indiya.

Kakakin kungiyar Yahya Sarea, ya bayyana cikin wata sanarwa da aka gabatar ta gidan talabijin na al-Masirah dake karkashin ikon kungiyar cewa, dakarunsu na ruwa sun kai hari na biyu kan jirgin Transworld Navigator a tekun Maliya da kwale-kwale mara matuki, wanda ya kai harin daidai kan jirgin ruwan.

Haka kuma, dakaru masu makamai masu linzami, sun kai hari kan jirgin ruwa mai suna Stolt Sequoia a tekun Indiya da tarin makamai masu linzami, yana mai bayyana hare-haren a matsayin wadanda suka cimma nasara.

A cewar kakakin, hare-haren wani martani ne ga keta haramcin da kungiyar ta yi wa jirage na shiga tashoshin ruwan Isra’ila.

Da yake tsokaci game da jirgin ruwan yaki na Eisenhower na Amurka da ya bar yankin ba da dadewa, Yahya ya yi ikirarin cewa, jerin hare-haren kungiyar ne suka kai jirgin ga tserewa. (Fa’iza Mustapha)