logo

HAUSA

Amondira, ‘yar kasar Thailand dake sha’awar koyon fasahar kayan kida na Zheng

2024-06-24 16:09:41 CMG Hausa

Kayan goge na Zheng, wani nau’in kayan kida ne na gargajiya na kabilar Han ta kasar Sin, wanda ke da tarihi na tsawon shekaru 2500 da wani abu. Saboda sauti mai dadin ji, da dimbin fasahohin da ake bukata wajen kadawa, da ma karfin nune-nune da wannan irin kayan kida yake da shi, ana kiran kayan goge na Zheng da "Sarkin Kayayyakin Kida" ko kuma "Fiyanon Gabas", wanda kuma ke iya bayyana falsafa da hikima ta kasar ta Sin. Amondira da ta zo daga kasar Thailand tana sha’awar kayan kida na Zheng tun tana karama, kuma tana fatan koyon fasahar kada wannan kayan kida. To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau za mu kawo muku labari ne game da wannan baiwar Allah mai suna Amondira.

Amondira ‘yar kasar Thailand, tana da wani suna na Sinanci Yang Liu. A halin yanzu tana karatun harshen Sinanci a sashen nazarin Sinanci na kasa da kasa na Jami'ar Harshe da Al'adu ta Beijing, ita kuma daliba ce a aji na biyu. A yayin da take ba da labarinta game da koyon fasahar kayan kida na Zheng, ta waiwayi cewa,

“Lokacin da nake makarantar sakandare a kasar Thailand, na taba koyon al'adu da tarihin kasar Sin, kuma malamanmu su kan yi magana kan tattalin arziki da ci gaban kasar Sin ta zamani.”

Yang Liu ta kara da cewa, gimbiyarsu ta Thailand, ita ma tana son al'adun kasar Sin sosai, kuma ta samu mataki na 10 a kan wasan kayan goge na Zheng. Don haka, lokacin da ta fara zuwa Jami'ar Harsuna da Al'adu ta Beijing, ta yi tambaya ko akwai darassin Zheng? Da ta san  cewa akwai darasin cikin jadawali, sai ta zabe shi ba tare da bata lokaci ba.

A karo na farko da Yang Liu ta kada kayan goge na Zheng, sauti mai dadi ya burge ta sosai. Ta yi duk kokarinta wajen koyon kada Zheng kuma ta sami karramawa daga malamarta, kuma bayan watanni uku kacal na karatu, Yang Liu ta samu damar kada kayan goge na Zheng a gaban masu kallo da yawa.

“Wannan kida ce da ke samun karbuwa a arewacin kasar Sin, wadda ta kasance wani sashe na shahararren kida ta gargajiyar kasar Sin mai suna ‘Tsawon Tsaunuka da Ruwa Masu Gudana’. Wannan kida na cike da kuzari, kuma da nishadi sosai.”

Yang Liu ta ce, ta kasance cikin fargaba a karon farko a dandalin wasan kwaikoyo, amma kuma ta samu yabo daga abokai da yawa na kasashen waje da na kasar Sin, lamarin da ya kara mata kwarin gwiwa sosai.

Ta hanyar koyon fasahar kayan goge na Zheng, Yang Liu ta kara fahimtar al'adun kasar Sin. Ta ce, kowane nau'i na kida yana ba da labari game da wasu abubuwa masu ban mamaki da suka faru a kasar Sin tun daga zamanin da har zuwa yanzu, wadanda suke nuna al'adun kasar ta Sin. Lokacin da ake jin sautin Zheng, ana kuma iya jin hikimar Sinawa.

“A gare ni, yayin da nake koyon Zheng, na fahimci al'adun Sinawa sosai. Kide-kide daban-daban suna da nasu labarai da hanyoyin bayyana ra'ayi daban daban.”

 Yang Liu ta kara da cewa, kade-kade na kudancin kasar Sin suna ba da nishadi, annashuwa, da nuna dan bacin rai, kamar dai natsuwa da 'yan kudancin kasar Sin ke nunawa, amma kade-kade na arewacin kasar suna sa mutane su ji farin ciki, cike da karfi da fara’a, kamar yadda jama'ar arewacin kasar suke nunawa.

Taken wakar "Kauna ta Rayuwa" na fim din "Tafiya zuwa Yamma" waka ce da Yang Liu ke kauna sosai, wadda ta bayyana labarai masu burge mutane sosai. Ta ce, a lokacin da ta kalli wannan fim din a kasar Thailand, ya yi matukar burge ta da kuma tunanin kan almara da labaran kasar Sin.

Yang Liu ta lura da cewa, ana ta kara samun shigowar kasar Sin a harkokin raya kasa da kasa, wannan wata babbar nasara ce ta hadin gwiwar Sin da kasashen duniya a sabon zamani. Ta ce, bayan nasarar da aka samu ta hanyar nuna goyon baya ga juna, da karfafa sada zumunci tsakanin kasashen Thailand da Sin, akwai wani irin karfi na fahimtar juna tsakanin jama'ar kasashen biyu.

“Duniya na bukatar hadin gwiwa a dukkan fannoni daga kanana zuwa manya, kasar Sin na kokarin taimaka wa juna da yin mu'amalar al'adu tare da kasashe da dama.”

Yang Liu ta bayyana cewa, tun lokacin da take karama, ta san cewa dangantakar da ke tsakanin Thailand da Sin tana da kyau sosai, tun daga gwamnati har zuwa al’umma. Ta hanyar ci gaba da yin karatu da nazari, ta kuma gano wasu abubuwan bai daya masu yawa tsakanin kasashen biyu. Ko da yake akwai bambance-bambance a wasu fannoni, amma kasashen biyu na iya nuna juriya da mutunta juna, wanda ke da muhimmanci sosai. Muna ta yin mu’ammalar al’adu, ana iya cewa, mu abokan juna ne na gaskiya.

Yang Liu ta kara da cewa, albarkatun ilimi masu inganci na kasar Sin, da kyautatuwar manufofi na bude kofa ga kasashen duniya, suna samar da wani dandali mai kyau ga daliban kasa da kasa don bude idanunsu kan duniya, ita ma za ta yi amfani da irin damar, don karfafa kwarewarta, da nufin taka rawarta wajen ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba.