Xi Jinping ya bayar da lambar yabo mafi girma a fannin kimiyya da fasaha ta kasar
2024-06-24 14:39:25 CMG Hausa
A yau Litinin, aka gudanar da babban taron kimiyya da fasaha na kasar Sin, da babban taron ba da lambar yabo a fagen kimiyya da fasaha na kasar, da ma babban taron kwalejoji biyu, wato kwalejin kimiyya ta kasar da kwalejin injiniya ta kasar, a nan birnin Beijing, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da lambar yabo ga wadanda suka cancanci samun lambar yabo mafi girma a fannin kimiyya da fasaha na kasar, tare da gabatar da muhimmin jawabi.
A cikin jawabinsa, Xi ya jaddada cewa, idan har kimiyya da fasaha za su bunkasa, to kasar za ta bunkasa, kuma idan kimiyya da fasaha suka yi karfi, kasar za ta yi karfi. Zamanantar da kimiyya da fasaha za ta taimaka wajen zamanantar da kasar Sin, kuma ingantacciyar ci gaba za ta dogara ne kan kirkirar kimiyya da fasaha don samar da sabbin karfin samar da hajoji da hidimomi. Dole ne mu amince da matsayin jagorancin kimiyya da fasaha bisa manyan tsare-tsare da muhimmiyar rawarsu, da himmantuwa wajen gina kasar Sin ta zama kasa mai karfi a fannin kimiyya da fasaha nan da shekarar 2035, da karfafa zayyana manyan matakai da tsare-tsare baki daya, da kuma hanzarta tabbatar da dogaro da kai a babban matakin kimiyya da fasaha.
Li Deren daga jami'ar Wuhan da kuma Xue Qikun daga jami'ar Tsinghua, su ne suka lashi lambar yabon mafi girma ta kimiyya da fasaha ta kasar Sin a shekarar 2023. (Bilkisu Xin)