logo

HAUSA

ANC: Jam’iyyun siyasa 10 za su shiga gwamnatin hadaka ta Afrika ta Kudu

2024-06-24 10:54:00 CMG Hausa

Jam’iyyar ANC mai mulkin Afrika ta Kudu, ta sanar da cewa, jam’iyyun siyasa 10 masu kujeru a majalisar dokokin kasar, sun amince da shiga gwamnatin hadaka ta GNU, wadda ANC din ke jagoranta.

Biyo bayan tattaunawa mai zafi da aka shafe makonni biyu ana yi, 10 daga cikin jam’iyyu 18 masu kujeru a majalisar dokokin kasar, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa gwamnatin hadaka, wadda ke bayyana aniyarsu ta hada hannu domin sanya muradun al’ummar kasar gaba da komai.

Jam’iyyun sun hada da ANC da Democratic Alliance da Patriotic Alliance da Inkatha Freedom da GOOD da Pan Africanist Congress of Azania da Vryheidsfront Plus da United Democratic Movement da Rise Mzansi da kuma Al Jama-ah.

A cewar ANC, gaba daya, jamiyyun sun samu kaso 70 na kuri’un da aka kada a zaben bana, wanda ke tabbatar da wakilcin bangarori da dama da kuduri mai karfi na shugabanci. Sun kuma amince da yin biyayya ga ka’idojin da aka zayyana cikin yarjejeniyar kafa gwamnatin da kuma hada hannu wajen cimma muradunsu. (Fa’iza Mustapha)