Tattalin arzikin Najeriya ya samu karuwar dala miliyan 5 daga cinikin gwal da kasar ta fara a kasuwannin duniya
2024-06-24 10:32:31 CMG Hausa
Najeriya ta samu tagomashi mai yawa a hada-hadar cinikin zallar madaral gwal da ta fara da kungiyar kasuwancin gwala-gwalai dake Burtaniya, wanda ya yi sanadin samun karuwar dala miliyan 5 a cikin asusun ajiyar kasar dake waje.
Ministan bunkasa harkokin ma’adanai na kasar Mr. Dele Alake ne ya tabbatar da hakan ranar Lahadi 23 ga wata a birnin Abuja lokacin da yake gabatarwa shugaba Tinubu samfurin sundukan danyen gwal din da aka hako a kasar.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Ministan ya ce, Najeriya ta kai tataccen gwal kilogram 70 zuwa kasuwar Landon Bullion, baya ga haka kuma an samu nasarar hako danyen gwal da ya baiwa gwamnati damar samun Naira biliyan 6 wanda aka yi amfani da su wajen gina tattalin arzikin yankunan karkara.
Ministan ma’adanan ya shaidawa shugaban na tarayyar Najeriya cewa, samfurin sundukan gwal da aka gabatar masa, kananan masu sana’ar hakar ma’adanai ne suka hako kuma asusun bunkasa ma’adanai ya tace su.
Mr. Dele Alake ya ce, za a sayarwa babban bankin kasa sundukan gwal din ne domin bunkasa asusun ajiyar Najeriya dake kasashen waje.
Ya ci gaba da bayanin cewa, Najeriya yanzu haka tana da kusan tan dubu dari 6 na zinare shimfide a jihohin kasar daban daban da suka hada da Zamfara da jihar Edo wanda aka kiyasta cewa, za su kai na dala biliyan 45.
A lokacin da yake duba tarin gwala-gwalan da aka baje a gabansa, shugaba na tarayyar Najeirya, Bola Ahmed Tinubu ya yabawa ma’aikatar ma’adanan bisa wannan kokari, inda ya bayyana cewa, fara cinikin gwal din a hukumance daya ne daga cikin nasarorin gwamnatinsa na fadada kafofin tattalin arziki maimakon mayar da hankali a kan bangare daya kacal. (Garba Abdullahi Bagwai)