logo

HAUSA

Kasar Sin ta bukaci Philippines da ta daina yaudarar duniya kan batun tekun kudancin Sin

2024-06-24 19:40:05 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin a yau Litinin ta bukaci kasar Philippines da ta daina tsokana, da yaudarar al’ummar duniya kan batun tekun kudancin kasar Sin.

Kalaman na ma’aikatar sun zo ne a matsayin martani ga ikirarin da shugaban kasar Philippines Ferdinand Romualdez Marcos ya yi a ranar Lahadin da ta gabata cewa, Manila za ta ci gaba da yin amfani a abin da ya kira ‘yanci da hakkinta kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada da kuma kare muradun kasar. (Yahaya)