logo

HAUSA

Sin da EU sun amince da tattaunawa kan yadda EU take binciken kin ba da tallafi kan EVs na kasar Sin

2024-06-23 16:13:32 CMG Hausa

A jiya Asabar ne ministan harkokin cinikayyar kasar Sin Wang Wentao, da mataimakin shugabar hukumar kungiyar Tarayyar Turai wato EU Valdis Dombrovskis, suka amince da fara shawarwari kan yadda EU take gudanar da bincike kan kin ba da tallafi kan motoci masu amfani da wutar lantarki na kasar Sin. Labarin da ma’aikatar cinikayyar Sin ta bayar ya ruwaito cewa, jami’an biyu sun cimma daidaito ta kafar bidiyo.

Da sanyin safiyar jiya Asabar ne Wang Wentao ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta yi tattaunawa da tuntubar juna kan motocin lantarki idan kungiyar EU ta amince da zama a teburin shawarwari bisa gaskiya. Wang ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da mataimakin shugaban gwamnatin kasar Jamus Robert Habeck.

Wang ya kara da cewa, kasar Sin a shirye take ta yi la'akari da damuwar bangarorin biyu cikin hikima da kwarewa, don kaucewa tabarbarewar matsalar cinikayyar.

A nasa bangare kuwa, Habeck ya yi imanin cewa, kakaba haraji shi ne hanya mafi muni domin hakan zai iya haifar da mummunar tabarbarewar matsalar cinikayya, yana mai jaddada cewa, tattaunawa da tuntubar juna ita ce hanya daya tilo ta warware matsaloli. (Yahaya)