logo

HAUSA

An gabatar da babi na biyu na rahoton nazarin lamuran ta’addanci na Xinjiang ta bakin wadanda suka tinkari ta’addancin

2024-06-23 20:53:16 CMG Hausa

A ranar 21 ga wannan wata, kwalejin nazarin watsa labaru da sarrafa harkokin yankunan iyakar kasa na jami’ar Jinan ya gabatar da babi na biyu na rahoton nazarin lamuran ta’addanci na jihar Xinjiang ta bakin mutanen da suka tinkari ta’addancin wato batun ta’addanci na dakin nishadi dake yankin Hotan na jihar Xinjiang da ya abku a ranar 15 ga watan Yunin shekarar 2014, wannan ne kashi na biyu na aikin mai  da hankali ga masu fama da lamuran ta’addanci da suka yi bayani kan lamuran ta bakinsu na farko a kasar Sin. Rahoton ya rubuta batutuwan da masu fama da ta’addanci suka fada, wanda ya shaida babbar illar da ta’addanci ya kawo wa kasar Sin, da cancantar a yi yaki da ta’addanci da kawar da tsattsauran ra’ayi a kasar. (Zainab Zhang)