logo

HAUSA

Shugaban DRC ya aza harsashin aikin tituna da kasar Sin za ta gina

2024-06-23 16:24:00 CMG Hausa

Shugaban kasar Congo (Kinshasa) Felix Tshisekedi a jiya Asabar ya aza harsashin aikin shimfida manyan hanyoyi mota a birnin Kinshasa, daya daga cikin ayyukan samar da muhimman ababen more rayuwa cikin kunshin shirin "albarkatu don ayyuka" tsakanin Congo (Kinshasa) da kasar Sin. Shugaba Tshisekedi ya ce, yana da kwarin gwiwa a kan fasahohin kasar Sin, yayin da yake fatan zurfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban a tsakanin kasashen biyu.

A ganin Alexis Gisaro Muvuni, karamin ministan samar da ababen more rayuwa da ayyukan jama'a na Congo (Kinshasa), wannan aikin ya nuna "sabon mataki" na hadin gwiwa tsakanin DRC da Sin. Kana ayyukan more rayuwa daban daban sun kyautata hadewar hanyoyi daban daban a kasar ta Congo (Kinshasa).

Wannan aikin zai ratsa unguwanni hudu na Kinshasa, inda mazauna fiye da miliyan 17 suke zama, tare da hanyoyi tara masu kutsawa da za su hade da mararraba hudu, hakan zai taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa. (Yahaya)