logo

HAUSA

Stückelberger: Amurka a ko da yaushe tana zabar ra’ayoyin da take so kan kare hakkin dan Adam don biyan bukatunta na siyasa

2024-06-23 17:12:27 CMG Hausa

Masani a harkokin kare hakkin dan Adam kuma babban daraktan gidauniyar Agape na Geneva, Christoph Stückelberger ya bayyana a kwanan baya cewa, akwai hujjoji da yawa da ke tabbatar da cewa, Amurka na zabar ra'ayoyin da take so kan kare hakkin bil'Adama don biyan muradunta na siyasa, kuma lokacin da wasu ra'ayoyin kare hakkin bil'Adama suka rinjayi muradunta na mulkin mallaka, Amurka sai ta yi watsi da su.

Da yake mayar da martani ga rubutacciyar hirar da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya yi da shi, Stückelberger ya ce, a halin da ake ciki a zirin Gaza, Amurka na fatan ci gaba da kiyaye matsayinta na abin da take kira "Mai kare hakkin bil'Adama" da "mai dabi'ar da za a yi koyi da shi", yayin da take ci gaba da samar da makamai da kayayyakin aiki ga Isra'ila, wanda shi ne daya daga cikin misalai masu yawa na matakan Amurka na nuna fuska biyu kan batun hakkin dan Adam.

Stückelberger, wanda ya kai ziyara kasar Sin sau da dama, ya jaddada cewa, kasar Sin a ko da yaushe tana mai da hankali kan yin hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban a karkashin tsarin MDD, yayin da Amurka ke jan kafa a wannan fanni. Ya bukaci kasashen yammacin duniya "kada su mai da abokan gaba da suke kokarin cin galaba a kansu shaidanu". Ya ce ba hikima ba ce a mai da batutuwan da suka shafi hakkin dan Adam makami. (Yahaya)