Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya ta bukaci yin gwajin kwaya ga ma’aurata kafin aure
2024-06-23 17:16:24 CMG Hausa
Shugaban hukumar yaki da sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA Birgediya Janaral Buba Marwa mai ritaya ya ce yanzu haka hukumar ta sanya batun gwajin kwaya ga ma’aurata kafin aure cikin shirye shiryenta na kawar da ta’ammali da miyagun kwayoyi a tsakanin al’ummar kasar.
Ya tabbatar da hakan ne ranar Juma’a 21 ga wata a babban masallacin birnin Abuja yayin addu’o’i na musamman a wani bangare na bikin ranar yaki da miyagun kwayoyi ta duniya na 2024, ya ce daman dai tuni hukumar ta gabatar da tsarin gwajin jini a tsakanin daliban manyan makarantun kasar.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Birgediya janaral Buba Marwa mai ritaya ya ce al’umma suna da rawar takawa wajen yaki da shan miyagun kwayoyi da kuma safararsa a Najeriya, a don haka ya bukaci iyaye da shugabannin al’umma da malaman addini da su bayar da kulawar da ta kamata ga dabi’un al’umominsu domin ganowa tare kuma da sanar da hukumar masu ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma dillalan kwayoyin.
Ya ce lokaci ya yi da limamai a masallatai da kuma shugabannin mujami’u su rinka fadakar da mabiyansu illar amfani da haramtattun kwayoyi, haka zalika akwai bukatar a sanya darussan da suke nuna kyama ga ta’ammali da miyagun kwayoyi cikin manhajar karatu.
“Mun karfafa yin gwajin kwayoyi ga daliban manyan makarantu da kuma ma’aurata kafin aure, wanda daman an saba ma’aurata kafin aure su kan gabatar da gwajin kwayar cutar HIV da kuma na jinsin jini, sannan kuma yanzu an bullo da tsarin yin gwajin kwaya ga ma’aurata kafin aure domin tabbatar da ganin an dakile shan miyagun kwayoyin a tsakanin ma’aurata da dalibai da kuma cigaba da yaduwar miyagun kwayoyin a tsakanin al’umma baki daya, lamarin da zai taimaka matuka wajen samar da iyali na gari mai cike da koshin lafiya.”(Garba Abdullahi Bagwai)