Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewa zuwa shekara ta 2025 za a kammala aikin shimfida bututun gas daga Ajaokuta zuwa Kano
2024-06-22 16:07:57 CMG Hausa
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za a kammala aikin binne bututun gas wanda ya taso daga Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano a karshen zango na uku na shekara ta 2025.
Ministan kudi Mr. Wale Edun ne ya tabbatar da hakan ranar Juma’a 21 ga wata lokacin da ya jagoranci ayarin ministoci biyu da kuma babban shugaban kamfanin mai na kasar Mele Kyari zuwa garin Kaduna domin duba matsayin aikin.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Ministan kudin yana tare ne da ministan yada labarai muhammad Idris da kuma karamin ministan albarkatun man fetur da iskar gas Hon Ekperikpe Ekpo, ya ce ba za a taba misalta mahimmancin aikin ba ga bunkasuwar tattalin arziki da na masana`antu a kasar.
“Wajibi ne mu yabawa dukkan wadanda suke da hannu wajen tabbatar da ganin cewa aikin shimfida bututun ya kai wannan matsayi na daf da kammaluwa”
Shi kuwa ministan yada labarai Muhammed Idris cewa yake nan ba da jimawa ba `yan Najeriya za su fara cin gajiya dari bisa dari na albarkatun iskar gas da ake da shi a Najeriya.
“Najeriya ba kasa ce kawai da take da arzikin man fetur ba kadai, kasa ce kuma da take da albarkatun gas, yanzu kuma muna cikin karnin da iskar gas ke da tasirin gaske a rayuwa.”
A nasa jawabin yayin rangadin, karamin minista a ma`aikatar albarkatun man fetur da iskar gas Hon. Ekpo ya ce aikin shimfida bututun zai bayar da damar alkinta dimbun albarkatun gas da ake da shi a Najeriya ta hanyar kyautata sha`anin samar da wutar lantarki, farfado da masana`antu da kuma samar da kafofin ayyukan yi.
“Muna kan aikin fadada wannan aiki zuwa sauran sassan kasa, a inda ake fatan zuwa karshen wa`adin wannan gwamnati za ta samar da iskar gas a kowacce jiha haka zalika za a samar da gas a kowanne gida.”
Kamfanin shimfida bututun man fetur na kasar China CPPECL da hadin gwiwa da kamfanin Brantex su ne suke gudanar da aikin mai tsawon kilomita 614.(Garba Abdullahi Bagwai)