Harajin da EU ta sanyawa motoci masu amfani da lantarki na kasar Sin, ita zai yi wa illa
2024-06-22 21:27:46 CMG Hausa
Hukumar kula da ayyukan raya kasa da gyare-gyare ta kasar Sin (NDRC), wadda ke zaman hukumar koli mai tsara tattalin arzikin kasar, ta bayyana a yau Asabar cewa, harajin da Tarayyar Turai (EU) ta sanyawa motoci masu amfani da lantarki na kasar Sin, ba zai amfanawa kowa da komai ba, tana mai cewa matakin illa zai yi ga EUn.
Shugaban hukumar Zheng Shanjie ne ya bayyana haka yayin taron tattaunawa na manyan jami’an Sin da Jamus karo na farko kan sauyin yanayi da amfani da makamashi mai tsafta, da ya gudana a Beijing.
Ya kara da cewa kariyar ciniki ba za ta amfanawa takara da komai ba, sai dai jinkirta yunkurin duniya na yaki da sauyin yanayi da inganta kiyaye muhalli da rage fitar da hayakin Carbon, inda ya bukaci Jamus ta jagoranci EU wajen yin abun da ya dace. (Fa’iza Mustapha)