logo

HAUSA

Robert Fitzthum, wanda ke bayyana ainihin labaran da ke faruwa a kasar Sin

2024-06-26 09:26:02 CRI

Labarin Nasarar Kasar Sin, sunan wani littafi ne game da yadda kasar Sin ta samu ci gabanta, sai dai da wuya a yi zaton bature ne  marubucinsa. Robert Fitzthum,shi ne marubucin littafin, dan kasar Austria ne, wanda tun shekarar 2013 ya zo kasar Sin ya fara zama a birnin Nanning, hedkwatar jihar Guangxi da ke kudancin kasar Sin. A cikin sama da shekaru 10 da yake rayuwa a kasar Sin, ya rubuta littattafai game da bunkasuwar kasar Sin bisa abubuwan da ya gani da ido. A cikin shirinmu na yau, bari mu gutsura muku labarinsa.