logo

HAUSA

‘Yan Nijar uku da aka kama a tashar Seme-Podji sun dawo gida

2024-06-21 21:29:22 CMG Hausa

Da kimanin karfe 6 na yammacin ranar jiya Alhamis, jirgin saman da ke dauke da ‘yan Nijar din uku, mataimakiyar darektan kamfanin Wacpo-Nijar da mataimakanta biyu, ya sauka a filin jiragen saman kasa da kasa na Hamani Diori da ke birnin Yamai.

Daga birnin Yamai, wakilinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Kafin zuwansu, gwamnan birnin Yamai ya gayyaci al’ummar birninsa da ta kebe babban tarbo ga wadannan ‘yan Nijar. Inda kuma duban mazauna birnin Yamai, yaro da babba, maza da mata suka fito dafifi domin tarbon ayarin motocin da ke rakiyar wadannan ma’aikatan kamfanin Wacpo-Niger a kan hanyar da ta taso daga filin jiragen sama har zuwa fadar shugaban kasa.

Wadannan ‘yan Nijar su ne, madam Moumouni Hadiza Ibra, mataimakiyar shugaban Wacpo-Niger, tare da abokan aikinta Ismael Cisse Ibrahim da Massoubaou Dan Kane, sun iso birnin Yamai cikin koshin lafiya, kuma cike da farin ciki .

Idan ba manta ba, ‘yan Nijar 5 jami’an ‘yan sandan kasar Benin suka kama a ranar 5 ga watan Yunin da muke ciki, sannan aka gabatar da su gaban kotun CRIET a ranar 13 ga wata, inda daga bisani aka saki biyu daga cikinsu. A ranar 17 ga wata, sauran ukun sun bayyana a gaban kotu. Kafin a sake saurarensu da yanke musu hukuncin zaman kason waje na watanin 18. Hukuncin da ya ba su damar dawowa kasarsu Nijar.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.