An kai karar American Airlines bisa laifin nuna wariyar launin fata
2024-06-21 13:48:20 CMG Hausa
Kwanan baya, kamfanin jiragen sama na kasar Amurka na American Airlines ya dakatar da wasu ma’aikatansa daga aiki ganin yadda suka kori wasu fasinjoji daga jirgin sama.
Rahotanni sun nuna cewa, ma’aikatan kamfanin sun kori wasu fasinjoji ‘yan asalin Afirka daga jiragen sama bisa dalilin yadda wani fasinja ya yi korafin cewa, ya ji warin jiki sosai cikin jirgin. Daga baya, fasinjoji guda uku daga cikin wadanda aka kora daga jirgin sun shigar da kara kan wannan batu a watan Mayun bana, inda suka bayyana cewa, an nuna musu wariyar launin fata. A cikin takardar karar, fasinjojin guda uku sun bayyana cewa, ba su san juna ba, kuma ba su zauna tare ba, kana an bukaci fasinjoji guda 8 gaba daya da su sauka daga jirgin saman.
Wannan ba shine karo na farko da aka kai karar American Airlines bisa laifin nuna wariyar launin fata ba. A shekarar 2017, kungiyar mutane masu launin fata ta kasar Amurka ta taba yi wa ‘yan asalin Afirka gargadi cewa, ya kamata su kauce wa hawan jiragen sama na kamfanin American Airlines, ganin yadda kamfanin ke nuna rashin mutun ci da kuma nuna wariyar launin fata. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)