Ministan Niger: Kullum Niger tana daukar Sin a matsayin abokiyar hadin kanta ta farko
2024-06-21 13:47:33 CMG Hausa
Jakadan Sin dake Niger Jiang Feng ya gana da ministan kula da harkokin sadarwa da wasiku da tattalin arzikin yanar gizo Sidi Mohamed Raliou, inda suka yi mu’ammala kan hadin gwiwar kimiyyar yanar gizo da yada labarai.
Sidi ya ce, kasashen biyu sun amince kuma suna goyon bayan juna, suna hadin gwiwarsu yadda ya kamata a fannoni daban-daban, musamman ma a fannin kimiyyar yanar gizo da yada labarai. Kullum Niger na daukar kasar Sin a matsayin abokiyar hadin kai kan matsaya daya, yana mai fatan kara hadin kai da yin mu’ammala da Sin.
A nasa bangare kuwa, Jiang Feng ya ce, Sin na fatan kara zurfafa hadin kai da Niger a wadannan bangarorin, ya karawa hukumomi da kamfanonin kasashen biyu kwarin gwiwar habaka hadin kansu, da ma ingiza samun ci gaba mai armashi ta yadda za a amfanawa al’umommin kasashen biyu. (Amina Xu)