Masanan MDD sun kalubalanci Amurka da sauran kasashen yammacin duniya da su dakatar da jigilar makamai zuwa Isra’ila
2024-06-21 11:23:29 CMG Hausa
Masanan MDD fiye da 30 sun bayar da hadaddiyar sanarwa a jiya 20 ga wannan wata a birnin Geneva dake kasar Switzerland cewa, aikin jigilar makamai zuwa Isra’ila ya sabawa dokokin kare hakkin dan Adam da jin kai na duniya, ya kamata kasashe da kamfanoni da abin ya shafa su dakatar da jigilar makamai zuwa Isra’ila nan da nan.
Kana sanarwar ta yi nuni da cewa, tilas ne a dakatar da jigilar makamai ta wata kasa ta daban, kuma hukumomin hada-hadar kudi da suka zuba jari ga kamfanonin samar da makaman su dauki alhakin wannan batu akansu. Sanarwar ta bayar da sunayen kamfanonin samar da makamai na kasar Amurka da kasashen Turai da kuma hukumomin hada-hadar kudi na kasashen yammacin duniya da dama. (Zainab Zhang)