Wakilin Sin ya yi kira da a yi amfani da intanet ta hanyoyin zaman lafiya
2024-06-21 13:42:18 CMG Hausa
Jiya Alhamis, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Fu Cong ya gabatar da jawabi a yayin taron tattaunawa kan batun tsaron intanet na kwamitin sulhu na MDD, inda ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su yi amfani da intanet ta hanyoyin zaman lafiya, tare da kiyaye tsaron amfani da intanet.
Fu ya ce, bunkasuwar zamantakewar al’umma ta dogara sosai kan haduwar intanet da al’ummomin duniyarmu, bai kamata a mai da intanet a matsayin sabon fagen yaki ba. Wasu kasashe sun mai da intanet a matsayin karfin sojansu, inda suke raya karfin sojansu ta intanet domin kafa kawancen intanet, tare kuma da kafa tsarin yake-yake ta intanet, lamarin da ya bata fahimtar juna a tsakanin kasa da kasa, kuma ya kawo barazana ga amfanin intanet, da kuma haddasa illa ga zaman lafiya da tsaron duniya.
Fu ya kara da cewa, cikin ‘yan shekarun nan, kasar Sin ta dukufa wajen yin shawarwari da musayar fasahohi da kasashe maso tasowa, domin inganta hadin gwiwa kan harkokin raya ababen more rayuwa, da raya fasahohi, da amfani da dokoki, da fuskantar harkokin gaggawa da sauransu, domin ba da gudummawa wajen daidaita harkokin intanet na kasa da kasa. Kana, kasar Sin a shirye take ta hada kai da gamayyar kasa da kasa wajen amfani da intanet cikin yanayin zaman lafiya da tsaro da hadin gwiwa, kuma bisa tsari mai inganci, a kokarin raya makomar bai daya a fannin amfani da intanet. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)