logo

HAUSA

An nada Michael Usi a matsayin sabon mataimakin shugaban kasar Malawi

2024-06-21 10:11:46 CMG Hausa

Ofishin kula da harkokin shugaban kasa da majalisar ministocin kasar Malawi ya bayar da sanarwa a jiya cewa, shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera ya nada Michael Usi a matsayin sabon mataimakinsa, wanda ya fara wa’adin aikinsa nan da nan. Michael Usi zai sha rantsuwar kama aiki a babban ginin majalisar dokokin kasar da misalin karfe 3 na yammacin ranar 21 ga wannan wata bisa agogon wuri.

An ce, Michael Usi shi ne ministan harkokin albarkatun halittu da tinkarar sauyin yanayi na kasar Malawi kafin aka nada shi a matsayin mataimakin shugaban kasar. (Zainab Zhang)