logo

HAUSA

Ba za’a iya warware matsalar ‘yan gudun hijira ba in har wasu kasashe sun ci gaba da nuna babakere

2024-06-20 20:24:29 CMG Hausa

Yau Alhamis 20 ga watan Yuni, rana ce ta ‘yan gudun-hijira ta duniya. Bisa rahoton da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, zuwa watan Mayun bana, adadin mutanen da aka tilastawa barin matsugunansu ya karu cikin jerin shekaru 12, wanda ya kai miliyan 120. Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a yau cewa, adadin ya nuna yadda rayukan al’umma ke salwanta, wanda ke kalubalantar zaman adalci a duniya da halayya ta kwarai ta dan Adam. Kakakin ya kuma jaddada cewa, matsalar ‘yan gudun-hijira, matsala ce da ta shafi sassan kasa da kasa, wadda ke bukatar hadin-gwiwar kasashe daban-daban don shawo kanta. Ba za’a iya warware matsalar ba, in dai wasu kasashe sun ci gaba da nuna babakere da fin karfinsu, da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe ta hanyar daukar matakan soja, gami da neman cimma muradunsu ta hanyar tada yake-yake.

Kaza lika, game da amincewar ma’aikatar harkokin wajen Amurka ga sayar wa Taiwan makamai, Lin Jian ya ce, kasar Sin na nuna matukar adawa gami da yin tir da batun, inda a cewarsa, batun yankin Taiwan, batu ne mai matukar muhimmanci a muhimman muradun kasar Sin, kana wani jan layi ne da ko ta yaya ba za’a iya tsallakewa ba a cikin dangantakar Sin da Amurka. Bai kamata a raina babbar manufar kasar Sin gami da karfinta, na nuna adawa ga masu yunkurin balle Taiwan daga babban yankin kasar, gami da kiyaye cikakken ‘yancin kasa da yankinta ba. (Murtala Zhang)