Nijeriya ta kaddamar da bincike kan malalar mai da ta auku a yankin Neja Delta
2024-06-20 09:39:49 CMG Hausa
Hukumomi a Nijeriya, sun kaddamar da bincike kan malalar mai daga wata rijiyar hakar man fetur dake jihar Bayelsa, mai arzikin mai, dake yankin Neja Delta.
A cewar shugaban hukumar kula da aikin gano malalar mai da kai dauki ta kasar Solomon Ukponevi, an gano yoyon ne ranar Litinin, a rijiya mai lamba 29 dake yankin Nembe na jihar, yayin aikin bincike da aka saba yi.
Solomon Ukponevi, ya shaidawa manema labarai cewa, an rufe rijiyar nan take, kuma tuni masu kai daukin gaggawa suka isa wurin domin daukar matakan da suka dace na shawo kan yoyon, yayin da aka kara tura sauran abubuwan da ake bukata wurin.
Ya ce hukumar gano malalar mai da kai dauki, ta riga ta tsara kai wata ziyarar bincike ta hadin gwiwa a yankin, domin tantance musabbabin malalar, da yawan danyen mai da ya malale da kuma tasirin da zai iya yi ga muhalli. (Fa’iza Mustapha)