Sin na goyon bayan kokarin kasashen Afrika na magance matsaloli ta hanyar da suka zaba
2024-06-20 10:43:00 CMG Hausa
Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Dai Bing, ya bayyana goyon bayan Sin ga kokarin da kasashen Afrika suke yi wajen warware matsalolinsu bisa hanyar da suka zaba.
Dai Bing ya bayyana haka ne a gun wani taron tattaunawa kan batun Libya da kwamitin sulhu na majalisar ya gudanar a jiya Laraba, inda ya ce ya yi imanin cewa, Libya za ta koyi darasi daga dabarun sulhu na kungiyar hadin kan kasashen Afrika wato AU, tare kuma da yin kira ga kasashen duniya da su ba da taimako idan akwai bukata.
Dai Bing ya kara da cewa, shawarwari ita ce hanya daya tilo ta magance rikicin Libya a siyasance. Kwanakin baya, babban taron wakilan jama’ar kasar da kwamitin kolin kasar Lybia sun kara tuntubar juna, da tattaunawa kan batun kafa gwamnatin bai daya da gudanar da zabe da dai sauran muhimman batutuwa. Ya ce Sin ta san cewa, bangori masu ruwa da tsaki a Libya za su yi shawarwari a siyasance karo na 2 a birnin Alkahira, hedkwatar kasar Masar. Kuma tana fatan za su nace ga hanyar da ta dace wato magance matsala a siyasance, da ci gaba da tuntubar juna da shawo kan bambancin ra’ayi da suka rage, da ma gaggauta aikin warware matsalar a siyasance. (Amina Xu)