logo

HAUSA

Zimbabwe na son hadin gwiwa da Sin wajen kare namun daji

2024-06-20 11:02:55 CMG Hausa

Mataimakin ministan kula da muhalli da yanayi da namun daji na kasar Zimbabwe John Paradza, ya ce a shirye kasarsa take ta hada gwiwa da Sin wajen kare namun daji da lalubo damarmakin raya tattalin arziki a bangaren.

John Paradza ya bayyana haka ne yayin wata rubutacciyar hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, inda ya ce Zimbabwe na da arzikin mabambantan halittu, wanda ke gabatar da tarin damarmakin hadin gwiwa tsakaninta da Sin.

Ya ce kasarsa za ta iya samun masu zuba jari dake son kare muhalli da za su iya hada hannu wajen inganta bude ido kan namun daji, saboda Sin na da babbar kasuwa. Kuma suna bukatar ci gaba da farfado da dukkan bangarorin tattalin arziki, ciki har da zuba jari a masana’antar namun daji.

A cewarsa, kare namun daji daya ne daga cikin muhimman bangarorin hadin gwiwa tsakanin Sin da Zimbabwe, kuma kasar Sin ta taimakawa Zimbabwe wajen inganta karfinta na kare namun dajin ta hanyar taimaka mata da horo da bincike da dabaru da kayayyakin yaki da farautar dabbobi ba bisa ka’ida ba. (Fa’iza Mustapha)