logo

HAUSA

Nijar ta dauki niyyar yaki da cutar sanyin kashi

2024-06-20 09:34:54 CMG Hausa

Kasar Nijar, kamar sauran kasashen duniya, ta yi bikin ranar kasa da kasa ta yaki da cutar sanyin kashi a ranar jiya Laraba 19 ga watan Junin shekarar 2024.  A albarkacin wannan rana da aka sallace ta bisa taken cutar sanyin kashi, a maganarta, ministan kiwon lafiya manjo kanal Garba Hakimi ya kira ga hada karfi da karfe domin yaki da wannan cuta.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

 

Ministan kiwon lafiya na kasar Nijar, dokta manjo kanal Garba Hakimi, cikin jawabinsa ta hanyar gidan rediyo da talabijin na kasa RTN, ya tabbatarwa ’yan Nijar cewa, wannan cuta ba za ta kasance mai tara marayu ba, dake haddasa mutuwar miliyoyin mutane. Ministan kiwon lafiya ya yi amfani da wannan dama domin yin kira ga abokan huldar kasar Nijar da su kara ba da goyon baya ga hukumomin kasa domin samun nasarar yaki da wannan annoba.

A cewar kungiyar kiwon lafiya ta duniya OMS, da ministan kiwon lafiya ya rawaito, kowace shekara yara dubu 300 ake aifuwa da wannan matsala, daga cikinsu dubu 200 a kasashen Afrika.

A cikin jawabinsa, ministan kiwon lafiya Garba Hakimi, ya jadadda cewa, Nijar na daga cikin kasashen Afrika dake fama da cutar sanyin kashi, inda kowace shekara kashi 5.11 cikin 100 na yara ake aifuwa da wannan cuta. Inda ya kara jaddada niyyar hukumomin kasar Nijar tare da na kiwon lafiya za su ci gaba da taimakawa da samar da magunguna ga cibiyar kula da masu fama da cutar sanyin kashi wajen daukar nauyin mutanen da ke fama da wannan cuta musammun ma yara da mata a duk fadin kasar Nijar.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar