Wakilin musamman na Xi Jinping ya halarci bikin rantsar da shugaban kasar Afirka ta Kudu
2024-06-20 20:26:18 CMG Hausa
A jiya Laraba 19 ga wata ne, bisa gayyatar Cyril Ramaphosa, wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana mataimakin shugaban kwamitin dindindin na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, Xiao Jie, ya halarci bikin rantsar da Ramaphosa a birnin Pretoria, inda kuma Ramaphosa ya yi sharwarwari da Xiao Jie.
Xiao ya mika sakon taya murna gami da bayyana fatan alheri na shugaba Xi Jinping zuwa ga Ramaphosa, tare da yi wa Ramaphosa fatan cimma sabbin nasarori a fannin raya kasa a sabon wa’adin aikinsa. Xiao ya ce, kasar Sin na matukar maida hankali wajen raya dangantaka tare da Afirka ta Kudu, kuma tana fatan yin kokari tare da sabuwar gwamnatin Afirka ta Kudu, domin kara samun fahimtar juna a fannin siyasa, da fadada hadin-gwiwa na zahiri, da ciyar da dangantakar kasashen biyu daga dukkan fannoni kuma bisa manyan tsare-tsare zuwa sabon matsayi. (Murtala Zhang)