Xi ya bukaci a kare muhallin tuddan Qinghai-Xizang da samar da ingantaccen ci gaba
2024-06-20 14:12:35 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin ci gaba da kokarin inganta kare muhallin tuddan Qinghai-Xizang, yayin rangadin da ya kai lardin Qinghai daga ranar Talata zuwa Laraba.
Xi Jinping wanda kuma shi ne sakatare janar na JKS kuma shugaban hukumar koli ta soji, ya kuma yi kira ga lardin da ya inganta samar da ci gaba mai inganci. (Fa’iza Mustapha)