Wakilin Sin ya yi bayani kan matsayin Sin kan kare hakkin dan Adam
2024-06-20 10:31:44 CMG Hausa
Zaunannen wakilin Sin dake ofishin MDD a Geneva da sauran kungiyoyin duniya dake kasar Switzerland Chen Xu, ya ce kasar Sin tana mai da hankali kan moriyar jama’a, da bin hanyar raya hakkin dan Adam dake dacewa da halin kasar, da kuma sa kaimi ga tabbatar da hakkin dan Adam a tsakanin kabilu daban daban na kasar, a yayin da take kokarin zamanintar da kanta.
Chen Xu ya bayyana haka ne jiya Laraba, lokacin da yake jawabi tare da bayyana matsayin kasar Sin, yayin gabatar da rahoton shekara kan kare hakkin dan Adam a gun taron majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 56.
A cikin jawabin, Chen Xu ya bayyana cewa, kasar Sin tana shiga ana damawa da ita cikin harkokin kare hakkin dan Adam na duniya, da goyon bayan ayyukan kare hakkin dan Adam na MDD, da yin shawarwari da kasa da kasa a wannan fanni. Haka kuma, ba ta amince da duk wani irin zargi mara tushe da ake yi mata ba, kana tana son hada hannu da ofishin kula da harkokin hakkin dan Adam na MDD da kasa da kasa, wajen sa kaimi ga raya sha’anin kare hakkin dan Adam bisa tushen girmama juna da tabbatar da adalci ga juna. (Zainab Zhang)