Ghana ta samu karuwar GDP da kashi 4.7 a rubu'in farko na 2024
2024-06-19 09:37:14 CMG Hausa
Hukumar kididdiga ta Ghana (GSS) ta sanar a jiya Talata cewa, yawan GDPn kasar Ghana ya karu da kashi 4.7 cikin dari a rubu'in farko na bana, wanda ya nuna karuwar kashi 0.5 cikin dari idan aka kwatanta da daidai lokacin a bara.
Samuel Kobina Annim, jami'in kididdiga na gwamnatin a hukumar ta GSS ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai, inda ya ce bangaren masana'antu ya samu karuwar da ta kai kashi 6.8 cikin dari, sai kuma bangaren noma ya samu karuwa ta kashi 4.1 cikin dari, yayin da bangaren ba da hidima ya karu da kashi 3.3 cikin dari.
"Muhimman abubuwan da suka haifar da karuwar GDPn a rubu'in farkon bana su ne sassan masana'antu na hakar ma'adinai, da fasa duwatsu, da gine-gine, da sassan hidima na bayanai da sadarwa, da ayyukan hidimar masauki da abinci, da kuma bangaren noma na amfanin gona," a cewar Annim.
Da ma gwamnatin Ghana ta yi hasashen samun karuwar GDP ta kashi 3.5 cikin dari a bana. (Yahaya)