logo

HAUSA

An bukaci Afirka da ta rungumi AI don samar da ci gaba da karfafa ma'aikatan nahiyar

2024-06-19 10:01:53 CMG Hausa

An bukaci nahiyar Afirka da ta yi amfani da damar da ke tattare da yin amfani da fasahar kwaikoyon tunanin dan Adam, wato AI a takaice, don bunkasa tattalin arzikinta da karfafa dimbin ma'aikata.

Hukumar raya kasashen Afirka ta kungiyar kasashen Afirka AU ta yi wannan kiran ne a wata takardar aiki mai suna "AI da makomar aiki a Afirka," wadda ta fitar ranar Talata. Ta ce fasahar AI za ta samar da kayan aiki mai karfi wajen tsara kyakkyawar makomar aiki a Afirka.

Takardar ta ce, ta hanyar tunkarar kalubale da kuma amfani da damar da ake samu, Afirka za ta iya yin amfani da AI don bunkasa tattalin arzikinta, da karfafa ma'aikatanta matasa, da kuma zama jagora wajen bunkasa kyakkyawar zamantakewar AI. Yawan matasa na Afirka da muhallin fasaha mai kuzari suna ba da damammaki masu mahimmanci wajen sanya nahiyar zama jagora a fannin fasahohin kirkire-kirkire da ci gaba mai dorewa. (Yahaya)