logo

HAUSA

Xi Jinping ya yi rangadi a lardin Qinghai

2024-06-19 11:15:59 CMG Hausa

 

Jiya Talata da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi rangadi a lardin Qinghai. Ya kai ziyarar a makarantar midil ta Xining dake jihar Guoluo mai cin gashin kanta ta kabilar Zang da haikalin Hongjue, don fahimtar yadda ake gaggauta hadin gwiwar yankin gabas da na yamma wajen ingiza sha’anin ba da ilmi da ba da taimako a wurin, da inganta tunanin ’yan uwan al’ummar kasar Sin na bai daya da habaka kyakkyawar tunanin yayata ruhin kishin kasa tsakanin mabiyan Budha mai asalin yankin Xizang (wato Tibet), har ma da yanayin ciyar da dunkulewar al’ummar Sin gaba. (Amina Xu)