logo

HAUSA

Yadda lardin Qinghai ya kasance

2024-06-19 21:36:09 CMG Hausa

Lardin Qinghai da ke arewa maso yammacin kasar Sin ke nan, wanda ya samu sunansa daga tabkin da ake kira Qinghai, wanda ya kasance tabki mai gishiri mafi girma na kasar Sin dake lardin. Lardin Qinghai na da matsakaicin tsayin mita 4058 daga leburin teku, wanda kuma ya kasance mafari na kogin Yangtse da rawayen kogi da ma kogin Lancang, don haka ma ake kiran lardin ma’adanar ruwa ta kasar Sin.