logo

HAUSA

Yaya Sin da Austriliya suke kiyaye dama mai yakini na raya huldarsu?

2024-06-19 14:04:00 CMG Hausa

 

Firaministan kasar Sin Li Qiang ya kai ziyarar aiki daga ran 15 zuwa 18 ga watan nan a kasar Australiya. Inda bangarorin biyu suka gabatar da “Sanarwa game da sakamakon taron shekara-shekara na ganawar firaministocin kasashen biyu cikin hadin kai”, kuma suka cimma matsaya daya kan hadin kansu a bangarorin tattalin arziki da cinikayya da al’adu da sauransu. Firaministan kasar Australiya Anthony Albanese ya nuna cewa, ziyarar takwaransa a wannan karo ta kara taka muhimmiyar rawa ga tabbatar da huldar kasashen biyu.

Bana ta cika shekaru 10 da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki a kasar Australiya da ma kafa huldar sada zumunta bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni tsakanin kasashen biyu. A cikin wadannan shekarun da suka gabata, huldarsu ta fuskanci sauye-sauye da kalubaloli sosai. Ta yaya za a kiyaye da kuma kara raya dama mai yakini da ake samu na bunkasa wannan hulda? Muhimman abubuwan da aka sa gaba su ne nacewa ga mutunta juna da hadin gwiwa tare da amincewa ga bambancin ra’ayi da kawo moriyar juna ta hadin kai.

A cikin ganawar tasu, bangaren Australiya ya bayyana matsayinsa na tsayin tsaya daka kan manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, ba zai goyi bayan an ware yankin Taiwan daga gare ta ba, kuma ba zai bar bambancin ra’ayi ya kawo cikas ga huldar kasashen biyu ba, kana da kara gaggauta kyautata raya huldarsu yadda ya kamata. In har bangarorin biyu za su so inganta tushen amincewa tsakaninsu, to ya zama dole a tabbatar da wadannan matakai.

A matsayin kasashe dake yankin Asiya da Pacific, Sin da Australiya ba su da ko wani rikici dake tsakaninsu ba, suna fahimtar juna a dimbin bangarori, ya kamata su yi zama cikin jituwa da hadin gwiwa don kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankalin shiyyar. Huldar dake tsakaninsu na samun kyautatuwa kuma tana kan hanyar da ta dace bayan sauye-sauye, dole ne a bunkasa hulda bisa hanya madaidaiciya da ake a kai yanzu, kuma su zama ’yan uwa na amincewa da juna da goyawa juna baya. Matakin da ba ma kawai ya dace da muradun bai daya na kasashen biyu ba, har ma ya kasance abin bukata ga shiyyar na kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali. (Amina Xu)