logo

HAUSA

Shugaban Rasha ya fara ziyarar aiki a kasar Koriya ta Arewa

2024-06-19 10:17:03 CMG Hausa

Yau Laraba, kamfanin dillancin labarai na KCNA na kasar Koriya ta Arewa ya fidda labari cewa, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya isa birnin Pyongyang, fadar mulkin kasar Koriya ta Arewa, inda ya kuma fara ziyararsa na aiki a kasar. Babban sakataren jam’iyya mai mulki ta kasar Koriya ta Arewa, kana, shugaban majalisar gudanarwar kasa Kim Jong-un ya tarbe shi a filin jiragen sama na kasa da kasa na Pyongyang domin maraba da zuwan shugaba Putin kasarsa.

Rahotanni na nuna cewa, Kim Jong-un ya ce, ya yi farin ciki sosai dangane da sake ganawarsa da shugaba Putin bayan kwanaki sama da 270. A nasa bangare kuma, Mista Putin ya nuna godiyarsa matuka ga Mista Kim ganin yadda ya tarbe shi a filin jiragen sama. Sa’an nan, sun je babban otel na Kumsusan, inda suka kuma yin shawarwari.

A watan Satumba na shekarar 2023, Kim Jong-un ya kai ziyarar aiki kasar Rasha, inda ya yi shawarwari masu muhimmanci da shugaba Putin a filin harba tauraron dan Adam na jihar Amurskaya dake gabas mai nisa a kasar Rasha. A yayin ganawarsu a wancan karo, shugabannin biyu sun tattauna kan hadin gwiwarsu kan manyan harkoki, inda suka kulla jarjejeniyoyi da kuma cimma matsaya daya. A lokacin kuma, shugaba Kim Jong-un ya gayyaci shugaba Putin da ya kawo ziyarar aiki kasar Koriya ta Arewa, shugaba Putin ya kuma karbi gayyatarsa. (Maryam Yang)