Yadda kasar Sin ke jagorantar yaki da kwararowar hamada a duniya
2024-06-19 07:40:31 CMG Hausa
Magance kwararowar hamada da gurbacewar kasa na da matukar muhimmanci don kiyaye wadatar abinci, da rage radadin talauci, da rage illa ga sauyin yanayi da bambancin halittu. An gabatar da hanyoyi da matakai da dama don magance kwararowar hamada tun bayan da ya dauki hankalin al'ummar duniya a taron Majalisar Dinkin Duniya kan kwararowar hamada ko (UNCOD) a takaice, a shekarar 1977. To a ranar Litinin ne aka gudanar da bikin ranar yaki da hamada da fari ta duniya ta bana, kuma babban kalubalen da ake fuskanta na lalacewar kasa da kwararowar hamada ya sake jan hankalin duniya.
Kasar Sin, daya daga cikin kasashen da ke fama da matsalar kwararowar hamada, ta samu gagarumin ci gaba wajen dakile bazuwar hamada bayan shekaru da dama da aka kwashe ana kokarin daidaita hamada ba tare da kakkautawa ba.
Hukumar kula da gandun daji da ciyayi ta kasar Sin ta bayyana cewa, daga shekarar 2009 zuwa 2019, hamadar kasar Sin ta ragu da murabba'in kilomita 50,000, hakan ya kasance wani gagarumin sauyi idan aka kwatanta da fadadar murabba'in kilomita 3,436 a karshen shekarar karnin da ya gabata. Ta yaya kasar Sin ta samu irin wannan gagarumar nasara? Kuma menene ma'anar nasarar da Sin ta samu kan kwararowar hamada ga duniya?,
Kimanin kashi 25 cikin 100 na fadin duniya ya lalace, wanda ke fitar da sinadarin carbon da nitrous oxide zuwa sararin samaniya, wanda hakan ya sa lalacewar kasa ta zama daya daga cikin muhimman abubuwan da ke taimakawa sauyin yanayi, Masana kimiyya sun yi gargadin cewa ana asarar ton biliyan 24 na kasa mai albarka a kowace shekara, musamman saboda rashin dorewar ayyukan noma, wanda idan aka ci gaba da yin hakan, na nufin kashi 95% na yankunan duniya na iya lalacewa nan da shekarar 2050. A duniya baki daya, mutane biliyan 3.2 ke fama da matsalar gurbacewar kasa, musamman al’ummomin karkara, manoma manya da kananan da kuma matalauta.
Yunkurin kasar Sin na yaki da kwararowar hamada ya fara ne tun a shekarar 1978 tare da kaddamar da shirin ba da mafaka na uku na arewa wato (TNSP), wanda kuma aka yiwa lakabi da babbar koriyar ganuwa. Aiki ne wanda aka tsara zai gudana daga shekarar 1978 zuwa 2050 a matakai takwas, wanda za a gina kantagar bishiyu don dakile yashin hamada, da shakar iskar Carbon Dioxide da hana zaizayar kasa a yanki mai fadin murabba'in kilomita 350,800 a larduna 13, tare da habaka gadun dajin kasar. (Sanusi Chen, Mohammed Yahaya, Faeza Mustapha)