logo

HAUSA

Li Qiang ya fara ziyarar aiki a Malaysia

2024-06-19 11:00:02 CMG Hausa

 

Jiya Talata, firaministan kasar Sin Li Qiang ya isa Kuala Lumpur, hedkwatar kasar Malaysia, inda ya fara zirayar aiki a kasar bisa gayyatar da takwaransa na kasar Datuk Seri Anwar Ibrahim ya yi masa.

Ministan sufuri na kasar Loke Siew Fook da jakadan Sin dake kasar Ouyang Yujing da dai sauran manyan jami’ai sun tarbe shi a filin saukar jiragen sama na Kuala Lumpur.

Li Qiang ya ce, a cikin shekaru 50 da suka gabata tun kafuwar huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu, huldarsu na samun bunkasuwa yadda ya kamata, har sun kara amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare, da habaka mu’ammalar al’adu, kana sun samu ci gaba mai armashi karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya”, lamarin dake amfanawa al’umomin kasashen biyu, kuma ya taka rawar gani ga zaman lafiya da bunkasuwar shiyyar. Sin na fatan kara hadin kai da Malaysia don kara tuntubar juna bisa manyan tsare-tsaren samun bunkasuwa da zurfafa moriyar juna ta hadin kai, da ma gaggauta mu’ammalar al’adu, ta yadda za a kafa kyakkyawar makomar kasashen biyu ta bai daya mai inganci, da ma taka karin rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunkasuwa da wadata a shiyyar da ma duk fadin duniya baki daya. (Amina Xu)