logo

HAUSA

Yankin Hong Kong na Sin ya kai matsayi na 5 a duniya a fannin karfin takara

2024-06-18 15:03:48 CMG Hausa

 

A cikin rahoton karfin takara a duniya na shekarar 2024 da kwalejin daidaita harkokin duniya da samun bunkasuwa na Switzerland wato IMD a takaice ya gabatar ba da dadewa ba, an ce yankin Hong Kong na kasar Sin ya daga matsayinsa daga 7 zuwa 5.

Wani mai magana da yawun yankin ya bayyana a yau Talata cewa, rahoton kwalejin IMD ya amince da ci gaba da mai da yankin Hong Kong daya daga cikin wasu yankuna mafi karfin tattalin arziki a duniya dake da ingantaccen karfin takara, bayan ya tattara da kuma nazari kan sahihan alkaluma da shawarwarin kungiyoyin kasuwancin duniya da dai sauransu. Yankin Hong Kong birni kacal a duniya dake hada fifikon Sin da na kasa da kasa bisa tsarin “kasa daya tsarin mulki biyu”, wanda ya dogaro da babban yankin kasar Sin ta tuntubar duk fadin duniya. Idan an yi hangen nesa, yankin zai ci gaba da taka rawar gani a matsayinsa mai tuntuba da mai kara samar damammaki, ta yadda tattalin arzikinsa zai kai sabon matsayi. (Amina Xu)