logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Taraba za ta biya sabon tsarin albashi da zarar gwamnatin tarayyar ta zartar

2024-06-18 09:09:59 CMG Hausa

Gwamnan jihar Taraba Mr Kefas Agbu ya kara jaddada kudurin gwamnatin jihar wajen ci gaba da kyautata rayuwar ma’aikata ta hanyar biyan dukkan hakkokinsu.

Ya tabbatar da hakan ne a farkon wannan makon lokacin da ya gudanar da wani rangadin duba wasu ayyukan raya kasa a sassan jihar daban daban. Ya ce ma’aikata su ne abokan ci gaba ta fuskar gudanuwar ayyukan gwamnati a don haka bai dace ba su rinka kokawa a ko da yaushe.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Gwamna Kefas ya ce, gwamnatin jihar ta Taraba ta shirya tsaf wajen ganin ma’aikatan jihar sun fara cin gajiyar sabon tsarin albashin da zarar gwamnatin tarayya da kungiyar kodago sun kammala cimma matsaya.

Ya ci gaba da cewa, nauyi ne da ya rataya a wuyansa kula da hakkin ma’aikata, a don haka koda nawa gwamnati da ’yan kodago suka cimma zai biya ma’aikatansa.

“Gwamnatin tarayya tana da burin kyautata rayuwar ma’aikata, haka ma yake a matakin jiha.”

Sai dai ya ce, ya zama wajibi ma’aikata su kasance masu rikon amanar aiki tare da kawar da lalaci a lokacin da suke gudanar da aikinsu. (Garba Abdullahi Bagwai)