Nzengue: Na cimma burina a kasar Sin!
2024-06-18 16:30:22 CMG Hausa
Wani dan kasar Gabon ya zo birnin Guangzhou daga Libreville, yana karatu da aiki a nan na tsawon shekaru talatin, yanzu yana aikin likita. Ya gane ma idanunsa yadda kasar Sin ke fadada bude kofa ga kasashen waje da samar da ci gaba, har ma ya cimma burinsa a nan. A cikin shirinmu na yau, bari mu ji labarin Jean Christian Nzengue, mu ga yadda ya cimma burinsa a kasar Sin.