logo

HAUSA

Sin ta bayyana matsayi da ra’ayinta a shawarwari kan hakkin bil Adam tsakaninta da Turai

2024-06-18 11:01:20 CMG Hausa

 

Jiya Litinin, mai ba da shawara ga ministan harkokin wajen kasar Sin Miao Deyu ya gana da mataimakiyar babban direktan hedkwatar sashin Asiya da Pacific ta hukumar gudanarwa ta EU Paola Pampaloni, wadda ta halarci shawarwari kan hakkin bil Adam tsakanin Sin da Turai da aka yi a birnin Beijing.

Miao Deyu ya yi bayyani kan matsayi da ci gaban da Sin ta samu wajen kare hakkin bil Adam, tare da nanata niyyar bautawa jama’a da JKS ta yi, kuma ana mai da zaman rayuwar jama’a wani burin da za a yi kokarin cimmawa, da ma tabbatar da kiyaye da raya muradun tushe na jama’a. Sin kuma ta ki yarda da siyasantar da kuma nuna fuska biyu kan batun hakkin bil Adam, da ma nuna adawa da tilastawa saura bin hanyar da ta zaba, kana da rashin jin dadi game da a tsoma baki cikin harkokin gidanta bisa hujjar hakkin bil Adam. Yana mai fatan bangarorin biyu za su kara yin mu’ammala da tuntubar juna don samun ci gaba tare, da taka rawar a zo a gani wajen daidaita harkokin hakkin bil Adam a duniya. Bangaren Turai ya bayyana burinsa na kara fahimtar kasar Sin ta amfani da wannan dama mai kyau, yana fatan kara hadin gwiwa da bangaren Sin a fannin kare hakkin bil Adam tsakanin mabambantan bangarorin.

A ranar 16 ga watan da muke ciki, babban direktan sashen kula da harkokin kasa da kasa na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Shen Bo da Paola Pampaloni sun shugabanci wani taron shawarwari kan batun hakkin bil Adama a birnin Chongqing na kasar Sin, inda bangaren Sin ya gabatar da hanyar da yake bi na kare hakkin bil Adam da matsayi da ci gaban da ya samu, da ma ra’ayin da yake da shi wajen daidaita harkokin hakkin bil Adam a duniya. Kana Mr. Shen Bo ya nuna rashin jin dadi game da abubuwan da suka shafi kasar Sin a cikin rahoton shekara-shekara kan hakkin bil Adam da demokuradiyyar kasa da kasa na shekarar 2023 da rahoto kan batun Hong kong da Macao, da EU ta fitar kwanan baya. Kuma Ya nanata cewa, batun yankin Xinjiang da Xizang (Tibet) da Hongkong harkokin cikin gidan kasar Sin ne, ba wanda ya isa ya tsoma baki a ciki. Ya nemi kasashen Turai da su mutunta gaskiya da hanyar da al’ummar Sinawa suka zaba da kansu, da kuma daina shisshigi cikin harkokin gidan kasar Sin bisa hujjar hakkin bil Adam. (Amina Xu)