logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Nijeriya zai kawo ziyara kasar Sin

2024-06-18 20:41:14 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen Nijeriya, Yusuf Maitama Tuggar, zai kawo ziyarar aiki kasar Sin daga ranar 19 zuwa 26 ga wata.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian ne ya sanar da haka a yau Talata.

A cewarsa, Tuggar zai ziyarci kasar Sin ne bisa gayyatarsa da takwaransa na kasar Sin Wang Yi ya yi, kuma yayin ziyarar, ministocin biyu za su jagoranci cikakken zama na farko na kwamitin gwamnatocin Sin da Nijeriya. (Fa’iza Mustapha)