Kasar Sin ta kaddamar da matakan gaggawa kan ambaliyar ruwa a larduna 3 da mamakon ruwan sama ya afkawa
2024-06-18 09:51:40 CMG Hausa
Hedkwatar yaki da ambaliyae ruwa da fari ta kasar Sin a ranar Litinin ta kaddamar da matakan gaggawa na IV na kandagarkin ambaliyar ruwa a larduna uku, bisa hasashen yiwuwar afkuwar ambaliyar ruwa, yayin da mamakon ruwan sama ke ci gaba da addabar kudancin kasar.
Yankunan da abin ya shafa sun hada da Guangdong, Hunan da Jiangxi. An samar da karin tawaga zuwa Guangdong don ba da taimako da jagoranci kan ayyukan rigakafin ambaliyar ruwan.
Hedkwatar tana ci gaba da aiwatar da matakan gaggawa na IV na shawo kan ambaliyar a lardunan Fujian, Guangxi, Zhejiang da Guizhou. (Yahaya)