Kamata ya yi NATO ta daina hura wutar rikicin Rasha da Ukraine
2024-06-18 21:07:15 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya ce, abin da ya kamata kungiyar NATO ta yi shi ne ta binciki kanta, maimakon shafawa kasar Sin bakin fenti kan rikicin Rasha da Ukraine.
Kakakin ya bayyana haka ne a yau Talata, a yayin taron manema labaru da aka saba yi kullum.
An ba da rahoton cewa, sakatare janar na kungiyar NATO Jens Stoltenberg ya yi gargadi a jiya Litinin, inda ya ce idan kasar Sin ta ci gaba da ba wa kasar Rasha fasahar soja, da kuma taimakawa kasar a rikicin da take da Ukraine, kasashen NATO za su sa kasar Sin ta "dandana kudarta".
Game da haka, Lin Jian ya kara da cewa, ba kasar Sin ce ta kirkira ko kuma ta shiga cikin rikicin na Ukraine ba, kuma a ko da yaushe tana himmantuwa wajen sa kaimi ga yin shawarwari cikin lumana, kana matsayin da kasar Sin ke dauka na adalci da gaskiya da muhimmiyar rawar da take takawa kan batun, na samun amincewa daga kasashen duniya.
Baya ga haka, dangane da ganawar da za a yi tsakanin 'yan majalisar dokokin Amurka da Dalai Lama, da kuma yadda Amurka ta zartar da wani kudurin doka mai alaka da Xizang, kakakin ya bayyana cewa, kasar Sin ta bukaci bangaren Amurka da ya mutunta kudurin da ya dauka na amincewa da Xizang a matsayin wani bangare na kasar Sin, kuma ba zai goyi bayan neman ‘yancin kan Xizang ba, haka kuma, kada ya rattaba hannu kan wancan kudurin doka. Ya ce kasar Sin za ta dauki kwararan matakai masu inganci don kare muradunta na mulkin kai, tsaro, da kuma ci gaba. (Bilkisu Xin)