logo

HAUSA

Xi ya bukaci a yi dukkan mai yiwuwa wajen yaki da ambaliya da fari

2024-06-18 20:35:46 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci a yi dukkan mai yiwuwa wajen yaki da ambaliya da fari, domin tabbatar da an yi kwakkwaran aiki wajen kare rayuka da kadarori da tabbatar da kwanciyar hankali.

Xi ya bayyana haka ne cikin umarnin da ya bayar game da ayyukan tunkarar ambaliya da fari.

Da yake tsokaci game da mamakon ruwan sama akai-akai a sassa da dama na kudancin kasar da fari a wasu yankunan arewaci, ya ce kada a yi kasa a gwiwa wajen bincike da ceton wadanda suka bata ko makale, kana a aiwatar da ingantaccen tsari domin wadanda iftila’i ya shafa da tabbatar da harkokin sun koma yadda suke da kuma rage asara.

Ya ce yayin da aka shiga lokacin aukuwar ambaliya a kasar Sin, ya kamata dukkan yankuna da sassa su inganta sa ido da bayar da gargadin wuri da shirya kayayyakin da ake bukata domin tunkarar dukkan bukatun gaggawa.

Larduna da dama na kasar Sin sun fara ko sun daukaka matakan agajin gaggawa domin tunkarar aukuwar ambaliya bayan fama da mamakon ruwan sama da cikar koguna. Haka kuma, ana fama da tsananin zafi a yankunan tsakiya da arewacin kasar, inda cibiyoyin kula da yanayi na kasar da dama ke ganin karuwar yanayin zafi da ya zarce wanda aka saba gani. (Fa’iza Mustapha)