logo

HAUSA

Firaministan Sin : Sin da Australiya al’umma ce ta kud da kud mai muradun bai daya

2024-06-18 15:02:41 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang ya bayyana a yau Talata cewa, Sin da Australiya suna cin gajiyar ci gaban juna, kuma al’umma ce ta kud da kud mai moriyar juna.

Firaministan Sin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake halartar taron tattaunawar shugabannin kamfanonin Sin da Australiya karo na 7 tare da firaministan Australiya Anthony Albanese.

Ya kuma kara da cewa, kasar Sin tana shirin daukar manyan matakai na kara zurfafa yin gyare-gyare a gida, da kara fadada bude kofar hukumomi ga ketare a kai a kai, kuma yanayin kasuwanci na kasar Sin zai kara samun kyautatuwa. (Yahaya)