logo

HAUSA

Firaministocin Sin da Austriliya sun gana da juna

2024-06-17 15:44:59 CMG Hausa

 

A safiyar yau Litinin a ginin majalisar dokokin kasar Austriliya dake Canberra, fadar mulkin kasar, an yi ganawar firaministocin kasashen Sin da Austriliya na shekara-shekara karo na 9, wato tsakanin Li Qiang da Anthony Albanese.

Li Qiang ya bayyana cewa, bana ta cika shekaru 10 da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi ziyarar aiki a kasar tare da kulla huldar sada zumunta bisa manyan tsare-tsare a duk fannoni tsakanin kasashen biyu. Idan an waiwayi bunkasuwar huldar kasashen biyu a cikin wadannan shekaru 10 da suka gabata, abin da aka mai da hankali a kai shi ne nacewa ga ka’idar mutunta juna da zaman tare da daidaita bambancin ra’ayi da hadin kai da kawowa juna moriya. Sin na fatan hadin kai da Austriliya don kiyaye da kara raya yanayi mai yakini na samun bunkasuwar huldar kasashen biyu, da kuma daukar wannan hulda zuwa wani sabon matsayi cikin hadin gwiwa, ta yadda za a amfanawa al’umommin kasashen biyu.

Li Qiang kuma ya kara da cewa, Sin na fatan kara hadin gwiwa da Austriliya cikin harkokin shiyya-shiyya da kasa da kasa, don kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin da muke ciki da kauracewa yaki da yin fito na fito tsakanin bangarori daban-daban da sabon nau’in yakin cacar baka, har ma da nacewa ga matsayin bude kofa da yin hakuri da juna da samun bunkasuwa tare da hadin gwiwa wajen ingiza raya tattalin arziki bisa tsarin bai daya, da raya tattalin arzikin duniya mai bude kofa.

A nasa bangare, Anthony Albanese ya ce, Austriliya na nacewa ga ka’idar “Kasar Sin daya tak a duniya”, ba za ta goyi bayan ware Taiwan daga gare ta ba. Kuma kasarsa na goyon bayan bunkasuwar Sin, tare da yabawa rawar gani da Sin take takawa wajen kawar da talauci a duniya. Yana mai fatan kara tuntubar kasar Sin, don taya murnar cika shekaru 10 da kafuwar huldar zumunci bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, da zurfafa hadin kai a fannonin zurfafa cinikayya da tattalin arziki da makamashi da al’adu da kiyaye muhalli da tinkarar sauyin yanayi da sauransu, ta yadda za a gaggauta kyautatuwa da bunkasuwar huldar kasashen biyu.

Firaministocin kasashen biyu sun amince da nacewa ga huldar dake takaninsu a yanzu, da tabbatar da yanayin bunkasuwar huldar yadda ya kamata da kuma kiyeye zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadatar shiyya-shiyya da kasa da kasa cikin hadin gwiwa. (Amina Xu)